Connect with us

News

Kungiyar Likitoci ta Kasa (NMA) ta sanar da janye aiki a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano 

Published

on

Advertisements
ads

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

A halin yanzu, shugabannin kungiyar likitocin Najeriya da kungiyar NAGGMDP ta yi kira da mambobinsu da su kwantar da hankalinsu sannan kuma wadanda ke aiki da asibitin kwararru na Murtala Muhammad da su dawo bakin aikinsu cikin gaggawa.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakatariyar NMA ta fitar bayan doguwar tattaunawa da CMD na cibiyar da babban sakataren hukumar HMB Kano da mai girma kwamishinan lafiya da kuma kwamishinan ‘yan sanda kan lamarin da ya faru a sashin masu kula da haihuwa na asibitin.

CBN ya fitar da dala miliyan 500 don biyan basussukan hada-hadar kudaden waje

Sakataren ya kara da cewa, “Za mu ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa tare da sanar da mambobinmu yadda ya kamata, Kwamishinan ‘yan sandan ya yi alkawarin tura ‘yan sanda cikin gaggawa zuwa sassan asibitin daban-daban, ya kuma yi alkawarin yin aiki tare da hukumar asibitin. da kuma HMB domin kamo wadanda suka aikata wannan danyen aikin domin

Sakataren zartarwa ya sake tabbatar wa tawagar ta NMA cewa daga yanzu mambobinsu za su kasance cikin koshin lafiya sannan kuma za a sanya dukkan kayan aiki da isasshen tsaro domin kaucewa sake afkuwar irin haka.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending