News
An kai Batun Rushe Masarautun Kano da Mayar da Sanusi Matsayin Sarkin Kano Gaban Majalisa Dokoki
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata kungiya mai suna “Yan Dangwalen Jihar Kano” ta rubutawa majalisar dokokin jihar Kano takardar neman rusa dokar kafa karin masarautu hudu da suka hadar da Gaya, Rano, Karaye da Bichi, wadanda gwamnatin da ta shude ta kafa, sannan sun nemi a maido da tsohon Sarkin Kano Sanusi II.
A wata wasika mai kwanan watan Fabrairu 5, 2024 da aike wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, wasikar na nuni da cewa a rusa masarautu tare da maido da Sanusi a matsayin sarkin Kano “zai samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano”
Yakamata Farashin Shinkafa Ya Daidaita Da Albashin Karamin Ma,aikaci A Mataki na Jiha
Wasikar tana cewa:
“Mun rubuto wasikar ne don rokon a wannan majalisa data yi gyara a dokar masarautun jihar kano, muna so a gyara dokar ta yadda za’a rushe sabbin masarautun da aka kirkira guda hudu.
“Mun yi imanin idan har aka hade masarautun suka koma masarauta daya za a fi samun hadin kai da cigaban al’ummar Kano. Rushe masarautun zai inganta zaman lafiya da tattalin arzikin jihar kano, don haka muke neman Wannan gida zai yi abun daya dace daidai da dok
Mun amince da ikon da Majalisar Dokokin Jihar Kano ke da shi kan harkokin tafiyar da masarautu.
“Duk da haka, cikin kaskantar da kai muna rokon majalissa da ta sake duba matakin tsige Sarki Sanusi Lamido Sanusi daga karagar mulki. Imaninmu ya ta’allaka ne a kan cewa mayar da shi kan karagar mulki za ta samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Kano .”
