Connect with us

News

HUKUMAR EFCC: Tshohon Gwamnan Jihar Kogi  zai gurfana kotu akan tuhumar sa da  zargin karkatar da Naira biliyan 80

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ƙasa da kwanaki bakwai bayan saukar kan mulki, bayan ya shafe wa’adin shekaru takwas ya na Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello zai gurfana kotu, domin tuhumar sa da zargin karkatar da Naira biliyan 80 daga aljihun gwamnati zuwa aljihun sa.

Advertisement

Yahaya Bello ya miƙa mulki ga Usman Ododo a ranar 27 ga Janairu.

Shugaba Tinubu ya isa Abuja bayan kammala ziyara a Faransa

Premium Times ta ruwaito cewa Hukumar EFCC ba ta damu ta gabatar wa kotu wasu sabbin tuhume-tuhume a kan Bello ba, sai kawai ta yi kwaskwarima kan cajin tuhume-tuhumen da kotu ke wa wani ɗan uwan tsohon gwamnan da makusancin sa, waɗanda kotu ke tuhuma kan zargin karkatar da biliyoyin nairorin Jihar Kogi.

Advertisement

Abin da kawai EFCC ta yi shi ne ɗora tuhume-tuhumen da ake wa Yahaya Bello a cikin waccan shari’a da ke gaban kotu.

A shari’ar dai ana tuhumar ƙanen Yahaya Bello mai suna Ali Bello da wani mutum mai suna Dauda Suleiman da laifin karkatar da kuɗaɗe.

Advertisement

 

To amma a cikin shari’ar yanzu an haɗa da Yahaya Bello, wanda shi kuma aka tuhume shi da zargin karkatar da Naira biliyan 80 zuwa aljifan sa. Adadin kuɗaɗen da EFCC ke nema a hannun da sun kai N80,246,470,089.88.

Advertisement

 

Tuhume-tuhumen sun nuna cewa abokin jidar kuɗaɗen mai suna Abdulsalami Hud, wanda Jami’in Kula da Harkokin Kuɗaɗe ne Gidan Gwamnatin Jihar Kogi, ya cika wandon sa da iska, ya gudu.

Advertisement

 

To sai dai kuma tuni har sabuwar Gwamnatin Jihar Kogi ta yi wa EFCC zazzafan raddin cewa bulkara da hauragiya ta ke yi, domin laifukan da ake cajin Yahaya Bello da aikatawa, ta ce an yi su ne tun wajen Satumba, 2015, lokacin Yahaya Bello bai ma zama gwamna ba.

Advertisement

 

Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, wanda kuma shi ne dai kwamishinan yaɗa labarai a mulkin Yahaya Bello, shi ne ya fito da bayanin da ke ƙunshe da raddin da gwamnatin ta Jihar Kogi ta yi wa EFCC.

Advertisement

 

Mutane da dama na mamakin gaggawar maka Yahaya Bello kotu, alhali ga irin su Bello Matawalle, maimakon a gurfanar da shi kamar yadda EFCC ta zarge shi, sai na aka naɗa Ƙaramin Ministan Tsaro.

Advertisement

 

Haka tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, shi ma maimakon a ji an ce EFCC ta yi cacukui da shi bayan saukar sa, sai ana naɗa shi Shugaban APC, jam’iyya mai mulki.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending