News
Zan Fasa Rumbunan Kayan Abinci Da Aka Ɓoye A Kano – Muhyi Rimin Gado
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaban hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da Rashawa ta jihar Kano Barista Muhyi Magaji Rimin Gado zai fara Kai ziyara runbunan ajiyar Kayan Abinci a Kano Dan fito da abincin da aka boye a sayarwa da jama’a.
Barista Muhyi Magaji Rimin Gado yace Haramin ne Kuma karya dokar kasa ne boye abinci Lokacin da ake tsanananin wahalar abinci a kasa .
Shugaba Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Fitar Da Hatsi Ton Dubu 42 Don Rage Tsadar Abinci A Nijeriya
Wakilinmu Amina Salisu Hamisu ya rawaito mana cewa Za’a fara Kai simanen Wuraren da ake zargi an boye kayan Abinci ne kafin watan Azumin Ramadan.
Muhyi Magaji Rimin Gado yace wajen da zasu fara Dira shine Kasuwar Dawanau inda yace duk Wanda aka kama ya boye abinci za’a fito da abincin a kaishi kasuwa ,wanda hakan Zai taimaka wajen sauko da farashin kayan Abinci.
Rimin Gado yace dokar kasa ta bashi dama na kodai ya fitar da kayan da aka boye zuwa kasuwa a sayar dasu ko ya kulle Rumbun ajiyar Kayan Abincin ya tafi Kotu