News
Shugaban Bankin Access da matar da Dansa sun yi hatsarin jirgin sama sun rasu
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani jirigin sama mai saukar Ungulu da ke dauke da shugaban bankin Access, Herbert Wigwe da wasu mutane biyar, ya yi hatsari a Jihar California ta Amurka, kuma duka Fasinjojinsa sun rasu
Jaridar new York time ta rawaito jirgin ya nufi Las Vegas ne lokacin da ya faɗo kusa da wani gari mai iyaka tsakanin Nevada da California a daren Juma’a.
Wigwe da matarsa da ɗansa suna cikin jirgin da ya yi hatsari ya faɗo a California kusa da iyakar Nevada.
Fasinjoji shida ne a cikin jirgin kuma babu wanda ya tsira. Gwamnatin Amurka ta tabbatar da mutuwar dukkan mutanen da ke cikin jirgin.