News
APC tayi rashin wasu daga cikin jogororin,ta zuwa babbar jam,iyyyar adawa ta NNPP

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan jihar kano Abba Kabir Yusuf ya karɓi wasu shugabannin kananan hukumomi guda 3 yan jam’iyyar APC da suka sauya Sheka zuwa jam’iyyar NNPP.
Gwamnan ya karbe su ne zuwa jam’iyyar NNPP a yau asabar din nan a gidan gwamnatin jihar Kano.
Jaridar goodevenig Nigeria ta rawaito cewar wadanda suka fita daga jam,iyyyar APC zuwa NNPP din kowanan,su babbaan kosa ne daga babbar jam,iyyyar adawar ta APC
Sunayaye
1. Nasarawa: Hon. Auwal Lawan Aramposu
2. Garin Malam: Mudassir Aliyu
3. Dawakin Tofa: Hon. Ado Tambai Kwa .
Sai mataimakin shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Hon. Garba Yahaya Labour .
Da yake jawabi gwamna Abba Kabir ya yabawa shugabannin kananan hukumomi bisa yadda suka yi watsi da jam’iyyar APC suka koma jam’iyyar NNPP.
Idan za’a iya tunawa jaridar indaranka ta rawaito cewar a farkon makon nan da muke bankwana da shi shugaban karamar hukumar Nasarawa Auwal Lawan Shu’aibu ya aiyana ficewar sa daga APC zuwa NNPP.
Kwanaki kadan ne dai suka ragewa dukkanin shugabannin kananan hukumomi na jihar Kano wa’adin mulkinsu ya kare.