News
Dauda lawan Ya Fara Biyan Garatuti Na Ma’aikatan Jiha Da Kananan Hukumomi

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin gwamna dauda lawan dare ta fara biyan bashin naira biliyan 13.4 na kudaden tallafi ga wadanda suka yi ritaya a jihar
Gwamnatin jihar ta kafa kwamiti don ya fara tantance bayanan ma’aikatan da suka yi ritaya don biyan basussukan garatuti daga shekarar 2011 zuwa yau.
Kakakin yada labaran Gwamnan Jihar, Sulaiman Bala Idris, ne ya bayyana haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a jihar.
A cewar takardar, wadanda suka yi ritaya da suke bin bashin garatuti tun daga shekara ta 2011 tuni suka fara karbar kudadensu.
“Gwamnatin jihar ta dauki wani muhimmin matakai na biyan basussukan da tsofaffin ma’aikatan da suka yi ritaya ke bi, da wadanda suka mutu. Cewarsa.