News
Hukumar EFCC Na Neman Matar Emefiele Da Wasu Mutum Uku Ruwa-A-Jallo
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta bayyana cewa tana neman Margaret Dumbiri Emefiele, wacce ita ce matar tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Haka kuma hukumar ta bayyana cewa, tana neman wani Eric Ocheme Odoh (namiji) da Jonathan Omoile (namiji) da kuma Anita Joy Omoile (mace) bisa tuhumar haɗa baki da tsohon gwamnan babban bankin ƙasar, wajen satar wasu maƙudan kuɗaɗe mallakin gwamnatin tarayya.
AFCON 2023: Tinubu zai halarci wasan karshe a ranar lahadi – Shugaban CAF, Motsepe
Hukumar ta EFCC, a cikin sanarwar da ta fitar ta kuma tuhumi wadanda ake nema da aikata laifukan da suka haɗa da samun kudi ta hanyar ƙarya da sata, wanda ya sabawa sashe na 411, 287 da 314 na dokar laifuka ta jihar Legas.”
Ta nemi masu bayanin inda waɗanda ake nema suke, da su tuntuɓi kowane ofishinta a Najeriya, ko su kira 08093322644.
Jaridar Inda Ranka ta ruwaito cewa a halin yanzu dai tsohon gwamnan na babban bankin na fuskantar shari’a kan tuhume-tuhume 20 da suka hada da bayar da cin hanci da rashawa, haɗa baki da cin amana da satar kuɗaɗen da suka kai dalar Amurka fiye da miliyan shida ($6,230,000.00).