News
Shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro su kai samame kan masu boye abinci
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI SALEH
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umurci hukumomin tsaron kasar nan da su hada kai da gwamnonin jihohi don yaki da ‘yan kasuwa masu dibi’ar boye kayan abinci.
Wannan na zuwa ne bayan taron da shugaban na Najeriya ya yi da gwamnonin jihohin kasar a wannan Alhamis, a game da matsalar karancin abinci da kasar ke fuskanta.
Hukumar Zaɓe ta Katsina ta sanar da ranar gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi
Shugaban ya mika wannan umurni ne kai tsaye ga mai ba shi shawara ta fannin tsaro, Nuhu Ribadu, babban sufeto Janar na ‘Yan Sandan kasar, Kayode Egbetokun, da kuma shugaban hukumar tsaro ta DSS, Yusuf Bichi.
Hankalin mahukuntan Najeriya ya tashi ne a kan wannan lamari, biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar Neja a makon da ya gabata a game da tsadar kayan abinci a kasar, wadda da dama suka alakanta lamarin da yadda ‘yan kasuwa ke boye abincin.
Wannan ne ma ya sa gwamnatin jihar Kano a kasar ta fara daukar mataki, domin ganin talakawanta sun samu sauki, inda ta kai samame wasu gidanjen ajiyar kayan abinci, bayan da aka tsegunta mata cewa an makare su da buhunan kayan abinci ana jira har sai sun yi tsada.
Batun tsadar abinci ya yi kamari a akasarin sassan Najeriya, wanda hakan ya sa wasu shugabannin al’umma su ke yi wa gwamnatin kasar kashedin cewa su dau matakan gaggawa, saboda ba su da abin da za su gaya wa mabiyansu don kwantar musu da hankali.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
