News
Ƴansanda sun kama mahaifin da ya kashe ɗansa saboda ya lakume abincinsa na dare
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Rundunar ƴansandar jihar Abia ta kama wani mahaifi mai suna Marcel Udeh bisa laifin kashe dansa.
Bisa ga wani bidiyo da ya kareda kafafen sada zumunta a yanar gizo da PREMIUM TIMES ta gani ya ce Udeh ya aikata haka a gidansa dake kauyen Eziama Lokpa-Ukwu dake karamar hukumar Umunneochi dake jihar ranar Litini da yamma .
Ƴan sanda Sun Saka Ladan Miliyan 50 Dan A Nemo Wasu Ƴan Bindiga
Mahaifin ya kashe dansa bayan ya dawo gida ya nemi abinci ya ci ya ga babu.
A cewar mahaifin ya nemi mutane su yi masa afuwa cewa hudubar shaidan ne ya bi.
Udeh ya ce dansa ya cinye sauran abincin da ya rage musu gabadaya dalilin da ya sa kawai ya kashe shi kenan.
Bayan ya kashe yaron ne mutane suka yi gaggawar kama shi suka daure kafafuwan sa da hannayensa domin kada ya gudu.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Maureen Chinaka ta tabbatar da wannan lamari a farkon makon jiya.
Chinaka ta ce Udeh na tsare a hannun su yayin da jami’an tsaron na gudanar da bincike akai.
Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandan ta bayyana cewa ‘yan sanda sun kama wani matashi Chinalu Ogbonna mai shekaru 27 da laifin kashe mahaifinsa Mmaduka Ogbonna mai shekaru 57.
Chinaka ta ce Chinalu ya kashe mahaifinsa ta hanyar shakeshi a gidansa dake layin Umueze a kauyen Amuzukwu dake karamar hukumar Umuahia ranar Litini da dare.
Ta ce yaron bayan ya kashe mahaifinsa ya kwakule idon mahaifinsa da sunan wai zai yi tafi da shi.
Chinaka ta ce Chinalu na tsare a ofishinsu sannan da zaran sun kammala bincike za su kai shi kotu domin yanke masa hukunci.
