Connect with us

News

Gwamnatin Tarayya Ta Fitar Da Jerin Sunayen Jihohi 14 Da Ka Iya Fuskantar Harin Ƴan Bindiga

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Gwamnatin Najeriya ta fitar da jerin jihohin kasar nan 14 da makarantun su ke cikin haɗari, dai-dai lokacin da ƴan bindiga ke ci gaba da kutsawa makarantu suna garkuwa da dalibai.

Shugabar hukumar kulawa da makarantu ta Najeriya Hajiya Halima Iliya ce ta bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a Abuja.

Zargin Cushen Kasafi: Ningi na fuskantar haɗarin dakatarwa daga Majalisa

Hajiya Halima Iliya ta ce jihohin sun haɗa da Adamawa, Bauchi, Borno, Benue, Yobe, Katsina, birnin tarayya Abuja, Kebbi, Sokoto, Plateau, Zamfara da karin wasu guda 3.

Bayanin hukumar na zuwa ne kasa da mako guda bayan da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da yara kusan 300 a jihar Kaduna, cikin su guda 28 sun tsere.

Advertisement

Kwana guda bayan nan kuma ‘yan bindigar suka sace daliban tsangaya 15 a jihar Sokoto

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending