News
Kira da data sun dawo daidai bayan katsewar wayoyin teku – HukumarNCC
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, NCC, ta ce an dawo da sabis din kira da na data bayan katsewar da wayoyin sadarwa su ka yi a ƙarƙashin teku.
Daraktan Hulda da Jama’a na Hukumar NCC, Dr Reuben Muoka, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin a Abuja.
Mista Muoka ya ce an maido da sabis din ne, biyo bayan katsewar da wayoyi su kayi a Teku a Cote de’Ivoire da Senegal a ranar 14 ga watan Maris, wanda ya haifar da matsalar kira da data.
“Muna farin cikin sanar da cewa a yanzu an maido da sabis zuwa kusan kashi 90 cikin 100 na mafi girman karfin amfani da su,” in ji shi.
Muoka ya ce dukkan kamfanonin sadarwa da matsalar ta shafa sun dauki gabaran gyara ta hanyar gyaran na karkashin ruwa ta hanyar amfani da wadanda basu katse ba.
-
News3 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion7 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News3 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
