News
Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi Ya kafa Hukumar Hana Cin Hanci da Rashawa
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi ya kafa Hukumar Sauraren Ƙorafe-ƙorafe, Hana Cin Hanci da Rashawa
Hukumar dai na ƙarƙashin shugaban ta na farko kenan Barista Salisu Abdu.
Sunan hukumar dai Jigawa State Public Complaints and Anti-Corruption Commission (JSPCACC). Wato Sauraren Ƙorafe-ƙorafe, Hana Cin Hanci da Rashawa
Hukumar NAFDAC ta haramta kai magunguna Sabon Gari da Niger Street a Kano
Cikin wata sanarwar da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Bala Ibrahim ya sa wa hannu, an naɗa Musa Uba-Auyo a matsayin Babban Sakataren Hukumar JSPCACC na l, sai kuma Hassan Hashim Babban Sakatare na ll.
Sanarwar ta ƙara da cewa Gwamna Namadi ya amince da naɗa Barista Yakubu Ibrahim a matsayin Sakataren JSPCACC, shi kuma Abdu-Zakari da Dakta Hadiya Aliyu mambobin hukumar.
Kamar yadda Sakataren Gwamnatin Jigawa ya bayyana a cikin sanarwar, ya ce “an naɗa su ne bayan da Majalisar Jihar Jigawa ta tantance su tare da amincewar ta domin naɗa su, yayin zaman ta na 118 a ranar Talata.
An haifi Barista Salisu Abdu a Gumel, cikin Ƙaramar Hukumar Gumel, a shekarar 1963. Tsohon ɗalibin Jami’ar Usman Ɗanfodiyo ta Sokoto ne.
Ya taɓa zama Daraktan Gabatar da Ƙararraki na Jihar Jigawa daga 2000 zuwa 2004.
Kuma ya taɓa zama mamba na Hukumar EFCC, mai wakiltar Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) daga 2022 zuwa 2023.
