Connect with us

News

Yajin Aiki: Mambobin Ƙungiyar SSANU Da NASU Sun Garƙame Kofar Shiga Jami’ar BUK

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Ƙungiyar manyan ma’aikatan Jami’oin Najeriya, SSANU da kuma ta ma’aikatan jami’a da basa koyarwa, NASU reshen jami’ar Bayero da ke Kano sun rufe Ƙofar shiga jami’ar a yajin aikin gargaɗi na kwana bakwai da suka soma.

Advertisement

Ma’aikatan na buƙatar Gwamnatin tarayya ta cika musu alƙawuran da ta yi musu.

Majalisar Wakilai Ta Amince Da Naira Tiriliyan 1.28 Kasafin Kuɗin Abuja

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ɗalibai ke jarrabawar a jami’ar lamarin da hana su samun shiga makarantar.

Advertisement

Wikki Time ta ruwaito cewa SSANU da NASU sun shiga yajin aikin na gargaɗi na kwana bakwai ne domin neman gwamnati ta biya musu wasu haƙƙoƙinsu.

Ciki har da rashin biyan albashinsu na wata 4 da gwamnatin ƙasar ba ta yi ba na lokacin da suka shiga yajin aiki na ƙasa baki ɗaya, a shekarar 2022.

Advertisement

Ƙungiyoyin sun nuna rashin jin daɗinsu kan rashin biyan mambobinsu albashin duk kuwa da cewa gwamnatin tarayya ta biya takwarorinsu na malaman jami’oi nasu kuɗaɗen.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending