News
Gwamnati Ta Dakatar Da Karɓar Kashi 25 Kan Motocin Da Aka Shigo Da Su Ba Bisa Ƙa’ida Ba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ministan Tattalin Arziki kuma mai sanyo ido kan fannin kuɗi, Mr. Wale Edun, ya unarci Hukumar Kwastom da ta dakatar da karɓar kashi 25 daga hannun masu shigo da motoci daga ƙetare ba bisa ƙa’ida ba.
Punch ta ruwaito cewa Kakakin hukumar na ƙasa, Abdullahi Maiwada, shi ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar a ranar Juma’a.
Najeriya ta zama fagen kashe-kashe ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu – Atiku Abubakar
Kwanan nan ne Gwamnatin Tarayya ta ba da sanarwar buɗe dama na tsawon kwana 90 don shigowa da wasu keɓaɓɓun motoci.
Blueprint ta ruwaito cewa da ma dai hukumar kan amshi kashi 25 kan motocin da aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba a matsayin ɓangare na dokar shigo da gwanjon motoci daga ƙetare kamar yadda dokar Destination Inspection Scheme in Nigeria (2013) da Dokar NCS ta 2023 suka tanada.
Sanarwar ta ce, “Domin rage raɗaɗin matsayin tattalin arziki tare da ƙarfafa wa jama’a gwiwa wajen bin doka, Ministan Tattalin Arziki kuma mai sanya ido kan fannin kuɗi, ya amince da a fakatar da kashi 25 da aka saba karɓa kan motocin da aka shigo da su ba bisa ƙa’ida ba.”
Daga nan, Maiwada ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a harkar shigo da motoci da sauransu da su yi amfani da wannan