News
Majalisar Dattawa Ta Bukaci A Haramta Shigo Da Tufafi Da Aka Kera A Kasashen Waje
Majalisar dattawan ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta haramta shigo da tufafi da aka saƙa a ƙasashen waje domin bunƙasa noman auduga da kuma farfaɗo da masana’antun yadi da suka durƙushe a Najeriya.
Yan majalisar sun ce ɗaukar wannan mataki zai ƙarfafa masana’antun cikin gida, ya tallafa wa manoman auduga, tare da dawo da martabar masana’antar yadi, musamman a yankin Kaduna da Kano, waɗanda a da suka kasance cibiyoyin samar da yadi a Najeriya.
An Cafke Matar Da Ta Yi Karyar Cewa ‘Yan Bindiga Sun Sace Ta A Dakin Otel Da Masoyinta
Majalisar ta kuma buƙaci Gwamnatin Tarayya, Ma’aikatar Noma da Ma’aikatar Kasuwanci da Zuba Jari su ɗauki matakan gaggawa domin farfaɗo da masana’antun yadin.
A cewar sanatocin, sake farfaɗo da wannan fanni zai samar da ayyukan yi ga miliyoyin yan Najeriya, musamman matasa, tare da rage zaman kashe wando da kuma taimakawa wajen shawo kan matsalolin tsaro.
Haka kuma, Majalisar ta buƙaci a ƙara kuɗaɗen tallafi na Bankin Masana’antu (BOI) tare da ware wani asusu na musamman domin tallafa wa masana’antun yadi da hanzarta farfaɗowarsu.
Sanatocin sun kuma jaddada muhimmancin ƙarfafa noman auduga a faɗin ƙasar, inda suka ce dorewar masana’antar yadi na da alaƙa kai tsaye da wadatar kayan masarufi, musamman auduga.
Sanata Sunday Marshall Katung ne ya gabatar da ƙudurin, tare da goyon bayan wasu sanatoci daga sassa daban-daban na ƙasar, ciki har da Adams Oshiomhole, Mohammed Tahir Monguno, Mustapha Khalid, Mustapha Khabeeb, Kawu Abdurrahman Suleiman, Simon Lalong, Aminu Waziri Tambuwal, Babangida Hussaini da Mohammed Dandutse.
