Connect with us

News

Ayyuka Bakawai Masu Tarin Lada A Kwana 10 Na Karshen Watan Ramadan —SheikhAmin Ibrahim Daurawa

Published

on

Spread the love

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

A yayin da aka shiga kwana goman karshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma.

Shahararren malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyawa Aminiya cewa riko da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su:

Advertisement

CBN Ya Yi Wa Bankuna Ƙarin Jarin Da Za Su Mallaka zuwa Naira biliyan 500. 

ITIKAFI: Ana so mutum idan mutum yana da hali ana ya shiga Itikafi, inda da lazimci bautar Allah. Mutum, namiji ko mace, na iya Itikafi na tsawon kwanakin ko na iya abin da ya sawwaka.

Neman daren Lailatul Kadar: Mutum ya dage wajen kirdado da neman dacewa da daren Lailatul Kadari, ta hanyar gabatar da salloli da addu’o’i da sauran ayyukan ibada, musamman a dararen mara a goman karshen watan Ramadan.

SALLAH: Musamman Sallar Tarawihi da Tahajjud, baya ga yin sallolin farilla a cikin jam’i, da kuma yin nafilolin da ake yi kafin ko bayan sallolin na farilla.

Advertisement

KARATUN AL-KUR’ANI: A dage a yawaita karatun Al-Kur’ani domin a cikin watan Ramadan aka saukar da shi, a daren Lailatul Kadar, cikin kwana goman karshe.

ADDU’O’I: A dage da addu’o’in neman garafa da rahamar Allah da aljannah da kuma dacewa da alherin duniya da lahira da kuma neman tsari daga wuta da kuma sharrin duniya da na lahira. Mutum na iya yin addu’a a lokutan da ake amsa addu’o’i kamar lokacin Sahur ko bude-bakin da lokacin da ake cikin azumin da cikin sujada ko a cikin sulusin karshe da dare da sauransu.

UMRAH: Hadisi ya nuna wanda ya yi Umra a cikin goman karshe na Ramadan zai samu ladar yin aikin Hajji tare da Manzon Allah (SAW).

Advertisement

ZAKKA: Ana so duk Musulmi mai hali ya fitar da Zakkar Kono ya ba wa mabukata. Magidanci da da da hali zai fitar da sa’i daya (Mudun Nabi hudu) na hatsi, haka kuma zai fitar wa iyalansa da duk wanda yake ciyarwa. Ana iya fitarwa a bayar daga ranar 28 ga Ramadan har zuwa lokacin tafiya masallacin idi ranar Karamar Sallah.

KABBARORI: Ana yin kabbarori daga bayan faduwar ranar jajibirin Karamar Sallah, har zuwa lokacin da za a idar da sallar idin.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *