Connect with us

News

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan

Published

on

FB IMG 1770849624495

A daidai lokacin da ya rage ‘yan kwanaki kaɗan a shiga watan Ramadan mai alfarma, mazauna jihar Kano na fuskantar tashin gwauron zabi na farashin kayan masarufi, musamman waɗanda ake amfani da su wajen shirya buɗa baki.

Wani bincike daaka gudanar a wasu manyan kasuwannin Kano, ciki har da Sheka da Rimi, ya nuna cewa farashin kayayyaki irin su zobo, tsamiya da kayan ƙamshi ya ƙaru da kusan kashi 60 cikin ɗari cikin makonni biyu kacal.

Advertisement

Tirela Ta Murkushe Mutum Biyu Har Lahira A Kaduna  ‎

Wasu ‘yan kasuwa sun danganta karin farashin da yawaitar buƙata a lokacin tunkarar Ramadan, tare da zargin cewa wasu manyan dillalai na ɓoye kaya domin sayar da su da tsada a gaba.

Advertisement

Nasiru Muhammad, wani ɗan kasuwa a kasuwar Sheka, ya ce tashin farashin ya fara ne tun kafin watan azumi ya karaso.

“Farashi ya bambanta sosai idan aka kwatanta da watan da ya gabata. Har ma ana sa ran zai ƙara tashi, domin wasu ‘yan kasuwa na ɓoye kaya don su sayar da su da tsada daga baya,” in ji shi.

Advertisement

Masu sayayya ma na bayyana damuwa kan yadda farashin kayayyaki ke ƙaruwa cikin gaggawa.

Amina Hamza, wata mai sayayya, ta ce farashin zobo ya tashi daga naira 1,200 zuwa naira 2,000 a cikin ɗan lokaci, yayin da ta ce ingancin kayan ma ya ragu.

Advertisement

Ta kuma ce farashin citta ya tashi daga naira 12,000 kan rabin kwano zuwa naira 14,000 cikin ƙasa da makonni biyu.

A kasuwar Rimi kuwa, wani mai sayar da kayan ƙamshi, Rabi’u Nakaka, ya ce farashin masoro ya tashi daga naira 2,500 zuwa naira 4,000 kan gwangwani ɗaya, yayin da tsamiya ma ta ƙaru sakamakon yawaitar buƙata domin yin kunun tsamiya a watan Ramadan.

Advertisement

Duk da cewa wasu ‘yan kasuwa na hasashen yiwuwar farashi ya lafa a tsakiyar watan azumi, sun gargadi cewa boye kaya da dillalai ke yi na iya ƙara tsananta matsin tattalin arziki ga al’umma.

Mazauna Kano dai na ci gaba da fatan hukumomi za su dauki matakan da za su rage tashin farashin, domin sauƙaƙa wa jama’a yayin da watan Ramadan ke gabatowa..

Advertisement

 

 

Advertisement

DAILYNews24 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending