News
Yadda Matar Aure Ta Rasu A Cikin Masallaci Yayin Tafsirin Ramadan
Wata matar aure mai suna Maman Zainab, mai shekaru 42, ta riga mu gidan gaskiya bayan da ta yanke jiki ta faɗi yayin tafsirin Ramadan a wani masallaci da ke Gawu, ƙaramar hukumar Abaji a Babban Birnin Tarayya (FCT).
Wani mazaunin yankin, Ismail Bala, ya shaida wa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:23 na safe a ranar Talata.
Masarautar Kano: Kotun Daukaka Kara Ta Dakatar Da Mayar Da Sanusi II A Matsayin Sarki
Maman Zainab ta bar gida cikin koshin lafiya tare da wasu mata uku daga makwabta domin halartar tafsirin Ramadan, amma yayin da take cikin masallaci, sai ta fara jin jiri da matsanancin ciwon kai.
Da take ƙoƙarin barin masallacin, sai ta yanke jiki ta faɗi. Duk da gaggawar kai ta asibitin Gawu Babangida, likitoci sun tabbatar da rasuwarta da zarar ta isa asibitin. Likitan da ya duba ta ya bayyana cewa ta rasu sakamakon hawan jini.
Lamarin ya girgiza jama’a a yankin, musamman mata masu halartar tafsirin Ramadan. An binne ta bisa koyarwar addinin Musulunci.
Allah ya jikanta da rahama, Ameen.
-
News4 days agoShekara Kwana: Shekaru 24 Kenan Da Hatsarin Jirgin Sama A Unguwar Gwammaja Dake Jihar Kano
-
News6 days agoKamfanonin Bada Bashi Ne Suka Cire N1.5bn Daga Albashin Ma’aikatan Kano — SSG
-
News4 days agoDr. Muhammed Musa Zango Ya Kaddamar Da Neman Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya A Jam’iyyar APC
