News
Rundunar ‘Yan Sanda Ta Kama Wasu Mutane 8 Da Ake Zargi Da Kashe Jami’anta A Delta
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce ta kama wasu mutane takwas da ake zargi da kashe jami’anta a wani bincike a yankin Ughelli da ke jihar Delta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.
Ya ce jami’an da ke aikin a ranar 23 ga watan Fabrairu, inda aka yi musu kwanton bauna wanda hakan ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda shida.
Shekara Guda Bayan Zaben Shakarar 2023: Har Yanzu Nijeriya Ba Ta Warware Ba
Adejobi ya ce kamen ya biyo bayan wani gagarumin bincike da jami’an ‘yan sandan suka yi.
Daily News24 ta ruwaito cewa an fara cafke mutane biyar da ake zargi jim kadan bayan faruwar lamarin yayin da aka kama wasu karin uku a wurare daban-daban.
Ya ce kama karin ukun ya biyo bayan kalamai ne da hadin kan wadanda aka kama da farko.
Adejobi ya ce a halin yanzu wadanda ake zargin suna hannun ‘yan sanda, inda suke taimakawa wajen gudanar da bincike.
Ya ce rundunar ‘yan sandan Najeriya ta dukufa wajen ganin an kama duk wadanda ke da hannu wajen aikata kisan kai da sauran laifuka makamantansu tare da gurfanar da su gaban kuliya cikin gaggawa.
Kakakin ‘yan sandan ya ce nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu, tare da kwararan hujjoji, da zarar an kammala bincike.