News
Tsohon Mataimakin Gwamnan Kwara ya rasu yana da shekara 74
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An bayyana rasuwar tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara Peter Kisira.
Gwamnatin jihar ce ta tabbatar da rasuwar marigayin cikin rasanarwar da ta fitar da safiyar Asabar ta bakin Babban Sakataren Yaɗa Labarai, Rafiu Ajakaye.
Marigayin ya bar duniya yana da shekara 74.
Kisira ya yi mataimakin Gwamnan Jihar ne a zamanin Gwamna Alhaji Abdulfattah Ahmed, daga watan Mayun 2011 zuwa Mayun 2019.
Tuni dai Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bayyana alhininsa kan rasuwar tare da miƙa ta’aziyya ga ‘yan uwan mamacin.