News
Mahaifi ya kai ɗansa kara ofishin ƴan sanda bisa zargin satar baburan mutane
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa jami’anta sun kama wani matashi da ya sato babur daga Babban Birnin Tarayya Abuja ya kawo shi jihar.
Kakakin rundunar Mansir Hassan wanda ya sanar da haka ranar Litini ya ce a ranar 29 ne wani mahaifi ya sanar da ‘yan sanda cewa yana zargin dan sa Sani Nafi’u ya sato babura daga Abuja.
Shugaba Tinubu Zai Halarci Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Senegal
Hassan ya ce bayan sun samu wannan bayani ne jami’an tsaron suka yi gaggawar kamo Sani wanda ke zama a kwatas din Tijjani Kaya a karamar hukumar Giwa.
Ya ce jami’an tsaron sun gano cewa Sani ya ji wa mai babur din da ya sato wani mai suna Shamsu Jamilu a Danja dake gundumar Kuje mai shekara 28 rauni sannan ya tafi da babur dinsa.
Premium Times ta ruwaito cewa Kakakin rundunar ya ce za a cigaba da gudanar da bincike akai domin gano wasu laifukan da matashin ya rika aikatawa a baya.