News
Shugaba Tinubu Zai Halarci Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Senegal
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shugaba kasa Bola Ahmad Tinubu zai bar Abuja, babban birnin Nijeriya domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye.
LEADERSHIP ta ta ruwaito cewa ana sa ran Tinubu zai bar Abuja a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu, 2024, zuwa Dakar, babban birnin Senegal.
El-Rufai: Nayi hasashen hakan zata faru – Shehu Sani kan bashin $350m
A cewar mai magana da yawun Tinubu, Ajuri Ngelale a ranar Litinin, shugaban da ya zama shugaba zai bi sahun sauran shugabannin duniya don halartar bikin rantsar da Diamniadio a ranar Talata.
Ya kara da cewa shugaban na Nijeriya zai samu rakiyar ministan harkokin waje, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar da wasu manyan jami’an gwamnati.
Sanarwar ta kara da cewa “Ana sa ran Tinubu zai dawo Nijeriya bayan kammala bikin rantsar da sabon shugaban kasar Senegal.”