Connect with us

News

Rundunar ‘Yan Sanda Ta Tsinci Gawar Wata Budurwa Mai Shekaru 14, A Ban Dakin Wani Otel 

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Rundunar ‘yan sandan jihar Bayelsa ta tsinci gawar wata budurwa mai shekaru 14, mai suna Shallon Ebitare a ban dakin wani otel dake Yenagoa.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa lamari ya auku ne ranar Laraba yayin da mamaciyar da saurayinta mai suna Lucky Okubo mai shekara 17 suka kama ɗaki a wani Otel don shakatawa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Musa Muhammed wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya ce yarinyar ta mutu a cikin ban ɗakin Otel ɗin.

Advertisement

Muhammed ya ce an yi hanzarin kai ta asibitin FMC dake Yenagoa amma likita ya tabbatar cewa ta rasu.

Ya ce ‘yan sanda sun kama Okubo bisa zargin kisa sannan Kwamishinan ‘yan sandan jihar, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin.

Advertisement

Zuwa yanzu Okubo na tsare a sashen SCID, Yenagoa yayin da ake ci gaba da bincike da nufin gano musabbabin mutuwar yarinyar.

Muhammed ya ce da zarar sun kammala binciken za su kai saurayin kotu domin yanke masa hukunci.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending