Sports
Real Madrid ta tsallake rijiya da baya a hannun Man City
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A cigaba da buga wasan cin kofin zakarun nahiyar turai da ake buga wa, a yau Talata kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta tsallake rijiya da baya yayin da Man city ta kusa tona mata asiri a filinta
Tun kafin a natsu cikin wasa Man City ta zura wa Madrid kwallo 1, abin da ya harzuka ƴan Madrid, nan da nan suka farke a cikin minti 12.
Wasa dai ta ɗau saiti sai duma ake yi ana dukar tamola, idan Man City ta zura kwallo, Madrid ta ramo.
Haka dai aka yi ta batakashi tsakanin kungiyoyin biyu.
Premium Times ta ruwaito cewa A minti 81 wato mintoci kafin a kammala wasa, Madrid ra farke kwallo ta uku da Man city ke cinta. Wasa ya zama 3-3 a gidan Madrid.
Yanzu Madrid za ta zo Ingila domin fafatawa da Man city aga cikin su wa zai kai ga buga wasan kusa da na karshe.