Sports
NLO: Kungiyar Barau FC na matakin farko a shiyyar Dutse A
DAGA MARYAM BASHIR MUSA
Kungiyar Kwallon kafa ta Barau Football Club, na matakin farko a shiyya ta farko wato Dutse ‘A’ a ci gaba da buga gasar Nationwide League One NLO ta kakar wasannin shekarar 2023/2024.
A wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar ta Barau FC Ahmad Hamisu Gwale ya turawa da Jaridar Inda Ranka a ranar Alhamis, ya ce duk da rashin nasara da kungiyar tayi a wasa na uku da ta buga da SBS FC a ranar Laraba da ci 1-0, Barau FC din ta ci gaba da kasancewa a matakin farko da maki Shida.
Kamfanonin Sadarwa A Nijeriya Na Neman Sahalewar Gwamnatin Domin Kara Kudin Kiran Waya.
Santar jihar Dutse da ke jihar Jigawa, na daya daga cikin Santocin da ake buga gasar NLO ta wannan shekarar, kuma kawo yanzu haka duka wasannin ukun an fafata su a shiyyar Dutse A.
Idan za a iya tunawa a wasan farko a filin wasa na Dutse, Barau FC ta doke Albarka FC da ci 2-1, sai kuma SBS FC tayi rashin nasara a hannun Sabon Gari 1-0, inda Ganduje Babies da Hausawa United suka raba maki.
A rana ta biyu kuwa, Barau FC ta sake samun nasara da ci 2-0 a kan Hausawa United, sai dai a wasa na Uku ne Barau FC tayi rashin nasara da ci 1-0 a hannun SBS FC a ranar Laraba.
Jumulla bayan kammala buga wasanni Uku a shiyyar ta Dutse A, Barau Football Club na matakin farko a gasar ta NLO da maki 6, sai SBS FC itama da maki 6 amma akwai banbacin kwallaye tsakaninsu.
Ganduje Babies na mataki na uku, sai Hausawa United mataki na 4 duka da maki iri daya wato maki Hudu, haka kuma Sabon Gari, mataki na 5 da maki 4, sai Albarka ta karse da maki 1.
Kawo yanzu haka a ranar Juma’a 26 ga Afrilun da muke ciki, Barau FC za ta buga da Ganduje Babies, Hausawa United da Sabon Gari, sai kuma SBS da Albarka FC.
Mai horar da kungiyar Barau Football Club Muhammad Yusha’u Madu, y bukaci yan wasan kungiyar su dage a sauran wasanni biyun da suka rage musu domin samun tikitin mataki na gaba.
Gasar Nationwide League One NLO ta kakar wasannin shekarar 2023/2024 na ci gaba da gudana a sauran Santocin da aka ware a fadin kasar nan, da ake saran Kungiyoyin da suka kammala a matakin farko zasu buga gasar Super 8.
