Sports
Liverpool Ta Dare Saman Teburin Gasar Premier
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kungiyar Liverpool ta Ingila ta dare saman teburin gasar Premier bayan da ta doke Sheffield da ci 3-1.
Sai dai Manchester United ta kara shiga rudani bayan da Chelsea ta lallasa ta da ci 4-3.
Shugaban Mulkin Sojan Nijar Ya Rusa Shugabancin Kananan Hukumomi
Wannan nasara da ‘yan wasan Jurgen Klopp suka samu ta nuna hobbasan da kocinsu ya yi da kuma tasirin Alexis Mac Allister, wanda kwallon da ya ci bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ta ba Liverpool nasara.
Yanzu Liverpool na da maki 70 yayin da Arsenal ke biye da ita da maki 68.
Man City kuma tana matki na uku da maki 67 Aston Villa ytake mataki na hudu da maki 59.
Yanzu Liverpool ta dawo da tagomashinta na kokarin lashe kofin na Premier yayin da United take fadowa kasa a gasar.