Sports
Real ta yi korafin alkalin wasa bai rubuta rahoton cin zarafi ba
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Real Madrid ta shigar da korafi cewar alkalin wasan da ya busa karawa da Osasuna a La Liga ranar Asabar, bai rubuta rahotan cin zarafin Vinicius Jr ba a rahotonsa.
Dan kwallon Brazil, Vinicius Jr na fuskantar cin zarafi da kalaman wariya a kaka uku a Sifaniya.
Real Madrid ta bukaci a dauki matakin da zai kawo karshen cin zarafin ‘yan kwallo a wasannin gasar Sifaniya.
An tuntubi kwamitin alkalan wasa na hukumar kwallon kafar Sifaniya don jin ko mai za su ce kan korafin Real Madrid.
Dan wasan mai shekara 23 ya zura kwallo biyu a raga a wasan da Real ta je ta ci 4-2 a karawar mako na 29 a La Liga ranar Asabar.
Hakan ya sa Real Madrid ta ci gaba da jan ragamar teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya da tazarar maki 8 tsakaninta da Barcelona ta biyu.
Real Madrid ta kara da ceawr tun ranar Juma’a ta rubuta korafi ga mahukuntan gasar tamaula ta Sifaniya kan cin zarafin da aka yi wa Vinicius a wajen magoya bayan Atletico da na Barcelona.
A wani bidiyo a kafar sada zumunta an nuna wani mai goyon bayan Atletico Madrid na rera wakar cin zarafin dan wasan Brazil a lokacin Champions League a karawa da Inter Milan ranar Laraba.
Haka kuma Real din ta ce irin wannan lamarin ya faru daga wajen wani mai goyon Barcelona a fafatawar da ta yi da Napoli a dai gasar ta zakarun Turai.
Dan wasan na tawagar Brazil na fama da fuskantar kalubalen kalaman wariya da na cin zarafi a filayen wasan tamaula a Sifaniya tsawon lokaci.
Ciki har da wanda aka yi masa a wasan hamayya da Atletico cikin Satumbar 2022, wanda aka ci zarafi kafin da kuma bayan tashi daga wasan.
A cikin watan kuma aka ci tarar mutum hudu £51,700 da dakatar da su shiga sitadiya shekara biyu, bayan da aka same su da laifin rataye butum-butumin Vinicius na cin zaragi kusa da filin da Real ke atisaye a Janairun 2024.
A kuma ranar aka ci tarar wasu magoya baya uku £4,300 da dakatar da su shiga sitadiya kaka daya, wadanda suka ci zarafin dan kwallon a wasa da Valencia cikin watan Mayu.
A kakar nan ta 2023/24 an bayar da rahoton cin zarafin Vinicius karo da dama, musamman a wasan Real a gidan Osasuna cikin Oktoba da a gidan Barcelona da kuma Valencia tun farkon watan nan