News
Ƙaramar Sallah: Kwamishinan Lafiya Ya Taya Gwamna Abba Kabir Yusuf Da Al’umma Musulmi Murna
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
An buƙaci Musulmi da su ci gaba da aiwatar da kyawawan halaye da darussan da suka koya a lokacin Azumin Ramadan da aka kammala.
Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ne ya yi wannan kiran a saƙonsa na Sallah ga al’ummar jihar cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar daga sashin hulda da jama’a na ma’aikatar tare da miƙawa manema labarai.
Kisan Soja 17 A Delta: Sojoji sun bankaɗo muggan makamai a gidan wani dillalin bindigogi
Dakta Labaran, wanda ya yi Sallar Idi a filin Idi na Ƙofar Mata tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi nuni da cewa tsoron Allah, ‘yan’uwantaka, juriya, ciyar da mabuƙata, addu’o’i, karatun Alƙur’ani da sauransu su ne abin da Musulmai suka yi riƙo da shi a cikin watan domin su samu kusanci ga Mahaliccinsu.
Ya kuma ƙara da cewa bayan kammala Azumin watan Ramadan, ana kyautata zaton mutane za su ci gaba da aiwatar da kyawawan ɗabi’u a sauran watannin shekara da nufin Allah ya gafarta musu zunubansu da suka gabata.
“A wannan rana mai girma, ina so a madadin iyalaina, ma’aikatar lafiya da hukumominta, in miƙa saƙon gaisuwata ga Mai Girma Gwamna, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ‘yan majalisar zartarwa ta jiha, da shugabancin babbar jam’iyyarmu, NNPP, da ɗaukacin al’ummar Kano kan gudanar da bukukuwan Sallah lafiya.
“Ina kuma miƙa saƙon girmamawa ga jagoranmu na siyasa, jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa kuma jigon tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso”, in ji shi.
Dakta Labaran ya yi nuni da cewa Gwamna Yusuf ya cancanci a yaba masa bisa yadda ya tausaya wa al’ummarsa a kowane ɓangare da ɗanye da dafaffen abinci a cikin watan Ramadan, inda ya jaddada cewa matakin ya taimaka matuƙa wajen sanya murmushi a fuskokin jama’a.
Dakta Labaran ya kuma yi kira gare su da su lura da yanayin lafiyarsu ta hanyar bin shawarwarin masana kiwon lafiya a kowane lokaci da kuma ziyartar wuraren kiwon lafiya a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso domin mai girma Gwamna yana yin duk mai yiwuwa wajen ƙara kuzari da sabunta tsarin kiwon lafiya a jihar.
