Sports
A Yau Za’a Kawo Karshen Cece-kuce Tsakanin Kungiyar Kallon Kafa Ta Manchester City Da Kuma Arsenal
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Da misalin karfe 4 na yammacin yau za’a fafata dukkannin wasan mako na 38 na gasa mai daraja ta daya ta kasar ingila wanda zai kawo karshen cece-kuce tsakanin kungiyar kallon kafa ta manchester city da kuma Arsenal.
Mancheater city itace ta daya gasar da maki 88, sai kungiyar kwallon kafa ta Arsernal wadda Arteta ke jagoranta da maki 86, wanda tazarar maki 2 ne tsakanin kungiyoyin guda biyu masu fatan lashe gasar.
Bayer Leverkusen Ta Zama Ta Farko Da Ta Buga Kakar Bundesliga Ba Tare Da Rashin Nasara Ba A Tarihi
Yazama dole kunguyar kwallon kafa ta Manchester city tayi nasara domin lashe gasar inda zata karbi bakwancin kungiyar kwallon kafa ta Westham a filin wasa na Al-ittihad wanda zai cika da dandazon magoya bayan kungiyar.
Itama kungiyara kwallon kafa ta Arsenal mai fatan ganin manchester city tayi tuntube a wasan na yau, zata karbi bakwancin kungiyar kwallon kafa ta Everton a filin wasa na Fly Emirate.
Arsenal tayi burin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham Hotspur data dakile manchester city na yunkurin lashe gasar amma abun yaci tira.
Afirimiyar, data gabata kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tayi yunkurin lashe gasar firimiyar kasar Ingila amma daga karshe manchester city tashiga gabansu kuma har tayi nasarar lashe gasar mai daraja ta farko a kasar ta Ingila.
Haka zalika a yau ma kungiyar ta arsenal koda tayi nasara akan Everton dole sai ta jira kungiyar kwallon kafa ta manchester city tayi rashin nasara sannan ta iya lashe gasar firimiyar, yayin da ita manchester city zata lashe kofi ne da zarar tayi nasara a wasan yau.
Shin ko yaya wasannin zasu kasan? Abun fada shine a jita lakaci wanda shine zaiyi alkalanci
