Sports
Manchester City Ta Lashe Gasar Firimiyar Kasar Ingila Karo Na 10 A Tarihi
DAGA UMMAR IBRAHIM HOTORO
Manchester city tayi nasarar doke kungiyar kwallon kafa ta westham da 3-1 a babban filin wasanta na Al-Ittihad ta hannun dan wasa phill poden wanda ya zura kwalleye 2 tare da kwallo guda daga dan wasa Rodri.
Kungiyar ta manchester city tana da jumilar maki 91 wadda tafi kowace kungiya yawan maki sae Arsenal mai fatan lashe kofin wadda ta kare a matsayin ta 2 a gasar ta wannan shekerar.
Shugaban Kasar Iran Ebrahim Raisi ya yi hatsarin jirgin sama
Itama kungiyar kwallon kafa ta Arsenal tayi nasara akan Everton da ci 2-1 amma duk da hakan hakansu bai cimma ruwa ba domin dai sun gaza lashe gasar da suke ta kokarin dauka.
Yanzu haka kungiyar ta manchester city tana da jumular kofunan firimiyar ta kasar Ingila guda 10 chif- chif, wanda hakan ka iya zama dama wajen shafe tarihin wasu kungiyoyin, musamman manyan kungiyoyin da aka dade ana fafatawa dasu.
Manchester city tayi rashin nasara a wasan kofin zakarun nahiyar turai akan kungiyar kwallon kafa ta Real madrid a bugun daga kai sai mai tsaron raga, amma yanzu a iya cewa kwalliya tabiya kudun sabulu.
-
News4 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News4 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
-
News2 days ago
Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano
