News
Kotu Ta Dakatar Da Rushe Masarautun Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da tube sarakuna biyar da rushe masarautunsu da gwamnatin jihar ta yi ranar Alhamis.
Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ya kuma dakatar da gwamnatin Kano da jami’an tsaro amfani da sabuwar dokar masarauntun jihar wadda aka yi wa gyaran fuska, Gwamna Abba Kabir ya sanya wa hannu a ranar.
Shugaba Tinubu ya ba da umarnin sake duba kwamitocin gudanarwar manyan makarantu
Umarnin wucin gadin dai ya shafi shugaban ’yan sanda da hukumar tsaro ta DSS da kuma Sibil Difens, har zuwa lokacin da za a kammala sauraron karar.
Sarkin Dawaki Babba Aminu Babba Danagundi, ne ya shigar da karar neman hana aiwatar da sabuwar dokar masarautun.
Sabuwar dokar ce ta kai ga dawo da Sarki Muhammadu Sanusi II a kujerar Sarkin Kano tare da kuma tsige Alhaji Aminu Ado Bayero da kujerar.
Hakazalika ta tube sarakunan sabbin masarutun Bichi, Gaya, Rano da Karaye wadanda tsohuwar Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro a shekarar 2019.
Kotun ta ba da umarnin cewa ba za a yi amfani da sabuwar dokar masarautun da aka yi wa garan fsuka ba har sai ta kammala sauraron karar.
Wadanda ake kara sun ha da Gwamnatin Kano, majalisar dokokin jihar da shugabanta, da kuma hukumomin tsaro da sauransu.
A ranar Alhamis bayan sanya hannu a kan sabuwar dokar ce Gwamna Abba ya sanar da dawo da Sarki Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano.
Gwamnan ya kuma ba wa sarakunan da aka rushe wa’adin sa’o’i 48 su fice daga fadar masarautun.
Share this:
-
News6 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News5 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News6 days ago
Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

