Connect with us

News

Mutum Bakwai Sun Mutu Sakamakon Hayaƙin Injin Janareto Da Ya Mamaye Ɗakin Da Suke Kwance

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Mutum bakwai sun mutu sakamakon hayaƙin injin janareto da ya mamaye ɗakin da suke kwance a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Advertisement

Jaridar Punch ta ruwaito cewa an samu gawarwakin mutanen galibinsu ɗaliban Jami’ar Neja Delta a cikin ɗakin Kiɗe-kiɗe watau ‘studio’ ranar Talata da safe, bayan sun shaƙi hayaƙin injin.

Jihar Kano Ce Kadai Ba A Aikin Cutar Yoyon Fitsari Kyauta A Najeriya —Baba Musa 

Jaridar ta ce sutudiyan na ɗaya daga cikin mutanen da suka mutun ne.

Advertisement

An ce a ranar Litinin da daddare ne marigayan suka fara aiki a sutudiyan, sai barci ya ɗauke su sakamakon gajiyar da suka yi, ba tare da sun kashe injin ba.

Jaridar ta ce ko da gari ya waye ranar Talata, sai aka samu gawar mutum shida daga cikinsu, yayin da ɗayan ke cikin mawuyacin hali inda nan take aka garzaya da shi asibiti, kafin shi ma ya rasu a asibitin.

Advertisement

Hayaƙin janareta dai na dauke da wani sinadari da ke toshe hanyoyin shaƙar iska, lamarin da ke barazana ga rayukan mutane.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending