Connect with us

News

Zanga-Zangar Neman Dawo Da Aminu Ado Bayero Karagar Mulki Ta Ɓarke A Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Magoya bayan Aminu Ado Bayero sun fara zanga-zanga a kan titin zuwa gidan gwamnatin Jihar Kano, inda suka buƙaci a mayar da tsohon sarkin kan karagar mulki.

Advertisement

Ana ci gaba da shiga ruɗani a Kano, yayin da jihar ke da sarakuna biyu, duk da rushe sarakunan da majalisar dokokin jihar ta yi a ranar Alhamis.

Bayan Shekara Guda A Mulki : Kungiyar SERAP Ta Buƙaci Tinubu Ya Bayyana Kadarorinsa

Da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Lahadi, matasa ɗauke da kwalaye suka mamaye tituna tare da buƙatar a dawo da Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano.

Advertisement

Wasu daga cikinsu sun ƙone tayoyi a kan tituna yayin da wasu ke rera waƙoƙin adawa da gwamnati.

Aminiya ta hangi ‘yan sanda a kan titunan amma ba su yi yunkurin tarwatsa masu zanga-zangar da ke tattaki zuwa fadar da Sarkin Sanusi II yake ba.

Advertisement

Masu zanga-zangar sun gudanar da salloli tare da addu’ar alƙunutu kafin daga bisani suka hau kan tituna don nuna rashin jin daɗinsu game da matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka.

Wasu daga cikinsu na riƙe da kwalaye ɗauke da rubuce-rubuce kamar haka: “Abba Kabir Yusuf, ka bi umarnin kotu”, “Kotu ce ta ba ka mulki”, “Dole ne ka yi biyayya ga kotu”, “Har yanzu Aminu ne sarkinmu”, “Muna adawa da rashin adalci.”

Advertisement

Idan ba a manta da sanyin safiyar ranar Lahadi ne, wasu gungun matasa suka gudanar da zanga-zanga a masarautar Gaya don n

una fushinsu kan rushe masarautar da aka yi.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending