Labarai
Mutane da dama sun rasa ransu sakamakon wani hari da ‘yan bindigo suka kai kasuwar kwanar Maro

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Mutane da dama sun rasa ransu sakamakon wani hari da ‘yan bindiga suka kai kasuwar kwanar Maro da ke mazabar Maro a yankin karamar hukumar Kajuru, jihar Kaduna.
Kajuru na daga cikin yankin jihar Kaduna da ‘yan bindiga suke yawan kai hari.
Da take tabbatar da kai harin, rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta sanar da cewa mutane biyar sun samu raunuka a yayin da mutum daya ya rasa ransa.
Sai dai, mazauna yankin sun sanar da manema labarai cewa a kalla mutane 12 ‘yan bindigar suka kasha sakamakon harin ‘yan bindigar, kamar yadda Channels Television ta rawaito.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari kasuwar da misalign karfe 4:30 na yammacin ranar Laraba tare da bude wuta kan jama’a ta kowanne bangare.
Ya bayyana cewa mutane biyar sun samu raunuka daban-daban a yayin da wani mutum guda ya rasa ransa tare da bayyana cewa rundunar ‘yan sanda na cigaba da gudanar da bincike domin tabbatar da yawan adadin mutanen da suka mutu.
A cewar Kakakin, jami’an rundunar ‘yan sanda da sauran tawagar jami’an tsaro sun garzaya zuwa kasuwar bayan samun kiran gaggawa tare da bayyana cewa yanzu haka suna bin sahun ‘yan bindigar domin kama su.
Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kawo harin ne daga dajin Kanwa na karamar hukumar Kajuru inda daya daga cikin sansaninsu yake,
-
Labarai6 days ago
Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Yi Wa Masu Digirin Ƙasashen Waje Jarrabawa
-
Labarai2 days ago
Jami’an Tsaro A Pakistan Sun Kama ’Yan Najeriya 20 Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi
-
Labarai2 days ago
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto
