News
Dan Sanda Ya Bindige Direba Kan Cin Hancin N200
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Wani dan shekara 40 da ‘ya’ya uku mai sana’ar kabu-kabu a cikin gari ya gamu da ajalinsa saboda ya hana ’yan sanda cin hancin Naira 200.
Dan sanda ya harbe direban ne a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.
Mummunan al’amarin ya faru ne a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu a kan hanyar Azikoro a cikin Yenagoa, da misalin karfe 8 na dare.
Rahotanni na nuni da cewa Lamarin ya janyo tofin Allah tsine daga jama’ar yankin da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’adama.
Rahotanni daga jihar Bayelsa na cewa har yanzu rundunar ’yan sandan jihar ba ta bayyana sunan jami’in da ya aika laifin ba.
cewa marigayin dan asalin kauyen Ayakoromo Bobougbene a Karamar Hukumar Burutu ne da ke zaune Yenagoa.
An ce, dan sandan ya bindige direban a cikin motarsa kirar Sienna ne yayin da yake dauke da fasinja daya a kujerar gaba.
Wasu mazauna unguwar da suka shaida faruwar lamarin sun ce, ’yan sandan da ke sintiri a kan titin sun tsayar da shi domin ya ba su Naira 200, kamar yadda suka saba karba a hannun masu ababen hawa.
Marigayin ya ce ba shi da shi a halin yanzu, nan take ’yar gardama ta shiga tsakaninsu, sai dan sandan ya saita shi ya bindige shi.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Bayelsa, ASP Musa Muhammed, ya ce nan gaba zai fitar da sanarwa kan lamarin.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
