Connect with us

News

ƙarancin albashi: Gwamnatin Tarraya ta yi wa NLC tayin N62,000

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamnatin Najeriya ta yi wa ƙungiyoyin ƙwadagon ƙasar tayin ba su naira 62,000 a matsayin mafi ƙanƙantar albashi maimakon naira 60,000 da ta yi musu tayi tun da farko.

Advertisement

Hakan na zuwa ne bayan shafe tsawon sa’o’i ɓangarorin biyu suna tattaunawa kan mafi ƙanƙantar albashin.

Hukumar NAFDAC Ta Gurfanar Da Masu Sayar Da Jabun Magunguna A Gaban  Kotu A Kano

A nata ɓangare ƙungiyar ƙwadagon ta rage buri zuwa naira 250,000, saɓanin naira 494,000 da a baya ta buƙaci gwamnatin ta bayar

Advertisement

A farkon makon nan ne gwamnatin ƙasar ta buƙaci ƙungiyar ƙwadagon ta janye yajin aikin da ta fara, bayan da gwamnatin ta alƙawarta yin ƙari kan naira 60,000 da ta yi a makon da ya gabata.

To amma tuni ƙungiyar gwamnonin ƙasar ta fitar da wata sanarwa da a ciki ta ce gwamnonin jihohin ƙasar ba za su iya biyan naira 60,000 ɗin da gwamnatin tarayyar ta yi tayin biyan ma’aikatan tun da farko ba.

Advertisement

Kawo yanzu dai ɓangarorin biyu sun tashi zaman ba tare da cimma matsaya ba, sai dai sun alƙawarta ci gaba da tattaunawar domin samun daidaito.

To sai dai ba a sani ba ko wannan motsi da duka ɓangarorin suka yi ka iya sa a cimma matsaya, don kauce wa komawa yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon za su iya shiga, lamarin da masana ke cewa zai iya haifar wa tattalin arzikin ƙasar koma baya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending