News
Hukumar Yaƙi Da Cin-hanci Ta Kano Ta Bankaɗo Badaƙalar Ɗaukar Aiki A Wasu Ma’aikatun Gwamnati
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta kama wasu mutane biyu tare da gayyatar wasu sakatarorin dindindin guda uku domin amsa tambayoyi kan badakalar sayar da fom din aiki a ofishin shugaban ma’aikata.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin-Gado, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa a Kano a jiya Laraba cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a badakalar.
Jaridun Najeriya: Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani A Safiyar Ranar Alhamis
Ya ce, tuni dubban masu neman aiki damfarar ta shafa.
“Bincike na farko ya gano ayyukan damfara a ofishin shugaban ma’aikata, hukumar ma’aikata, hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar Kano, da hukumar kula da harkokin kiwon lafiya.
“Mutane biyun da ake zargin da ake tsare da su suna bayar da hadin kai ga binciken, wanda ya kai ga rufe shafin ɗaukar aikin na bogi.
“Hukumar tana kokarin kawar da cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da an yi adalci a badakalar neman aikin yi da ta damfari dubban masu neman aiki,” in ji Rimin-Gado.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
