News
Jaridun Najeriya: Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani A Safiyar Ranar Alhamis
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
1. Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta bayyana cewa kungiyoyin kwadago ba su amince da wani takamaiman adadi a matsayin sabon mafi karancin albashi ba. Kungiyar ta NLC dai na mayar da martani ne kan ikirarin da shugaba Bola Tinubu ya yi na cewa an cimma matsaya kan sabon mafi karancin albashi na kasa.
2. Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya rubutawa kwamishinan ‘yan sanda na Kano takarda, inda ya bukaci a samar masa da tsaro na musamman domin bukukuwan Sallah mai zuwa. Wannan na kunshe ne a cikin wata wasika mai dauke da lamba Ref: HRH/ADM/06/1/217, mai kwanan wata 10 ga watan Yunin 2024, kuma Sakataren Mai Zaman Kansa na Sarki ya sanya wa hannu.
Wasan Ɓuya Ya Ƙare Hukumar EFCC ZA Ta Gurfanar Da Yahaya Bello A Kotu
3. Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa (Arewa-maso-Yamma) Salihu Mohammed Lukman, ya yi murabus daga jam’iyyar. Lukman, wanda tsohon mamba ne a kwamitin gudanarwa na jam’iyyar (NWC), ya bayyana a ranar Larabar da ta gabata cewa ya fice daga jam’iyyar ne saboda “rashin tsarin dimokuradiyya na cikin gida” da kuma zargin gazawar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen ba da damar kawo gyara a cikin jam’iyyar.
4. Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya yi zargin cewa wasu gwamnonin jihohi suna karfafa masu aikata laifuka don amfani da siyasa, maimakon bunkasar kwararrun ma’aikatan gwamnati. Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Benin yayin da yake kaddamar da sakatariyar jihar da Gwamna Godwin Obaseki ya gyara.
5. Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben shekarar da ta gabata, Peter Obi, ya bayyana cewa Najeriya ba ta bin tafarkin dimokuradiyya na gaskiya, kuma ta koma mulkin kama-karya da kuma mulkin gargajiya. Ya kara da cewa gazawar shugabanci ya haifar da cin hanci da rashawa na tsari, da rashin tsaro da yawa, rashin ‘yancin fadin albarkacin baki, karuwar talauci, da yunwa da wahala da ba a taba ganin irinsa ba.
6. Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya bukaci likitocin Najeriya masu neman kwarewa da su ci gaba da zama a kasar tare da marawa gwamnatin shugaba Bola Tinubu baya wajen inganta harkokin kiwon lafiya. Ya ce idan likitoci suka bijirewa jarabawar neman wuraren kiwo a kasashen waje, za su gane cewa shugaba Tinubu na da muradin su a zuciya.
7. Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da bukatar da shugaban masu fafutukar kafa kasar Biyafara (IPOB) Nnamdi Kanu da ake tsare da shi ya shigar na neman kotu ta ba shi izinin kalubalantar umarnin da ya haramta kungiyar. A hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, ta tabbatar da hujjar da lauyan gwamnatin tarayya, Oyin Koleosho ya yi na cewa bukatar da lauyan Kanu Alloy Ejimakor ya shigar a madadin wanda ake tsare da shi bai dace ba.
8. Ofishin shugaban ma’aikata ya dakatar da babban sakatare a ma’aikatar harkokin wajen kasar, Ambasada Ibrahim Lamuwa bisa zargin cin zarafi. Shugabar ma’aikatan, Folashade Yemi-Esan, ta ce za a dakatar da babban sakataren ne har sai an kammala bincike kan zargin da ake masa.
9. Hukumar Yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) a ranar Larabar da ta gabata ta ce tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, wanda ake zargi da damfarar Tsabar Kudi har Naira biliyan N80.2bn, ya yi wa tsarin shari’ar Najeriya ba’a, inda ya kasa gabatar da kansa a gaban kotu. Mukaddashin daraktan hukumar EFCC na shiyyar Benin, Mista Effa Okim, ya bayyana hakan a wata ziyarar sanin makamar aiki da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen jihar Delta a Asaba, babban birnin jihar Delta ta kai masa.
10. Wata babbar kotun jihar Delta dake zamanta a Asaba a ranar Talata ta yankewa Insifekto Ubi Ebri na rundunar ‘yan sandan Najeriya hukuncin kisa bisa samun sa da laifin kisan kai. Kotun da ke karkashin mai shari’a C. D. Diai, ta yanke wa Insifekton hukuncin kisa bisa laifin kashe wani dillalin waya, Mista Onyeka Ibeh, a Asaba.
