News
Kotu Ta Dage Lokacin Da Za Ta Yanke Hukunci Kan Rikicin Masarautar Kano Zuwa Nan Da ‘Yan Sa’o’i Kaɗan
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wata babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta mayar da karfe 2 na rana a matsayin lokacin da za ta yanke hukunci kan dokar rushe sarakuna a Jihar Kano.
Tun da farko dai an tsayar da lokacin yanke hukunci da karfe 12 na Rana, amma daga bisani an sanar da sauya lokacin ne kafin cikar wa,adin na farko.
Fadan Daba Ya Haifar Da Zaman Dardar A Unguwanne Da Dama A Cikin Kano.
Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf ne dai ya yi amfani da dokar wajen tsige Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero da kuma sauya tsarin kafa masarautu huɗu Bichi, da Rano, da Karaye, da Gaya, wanda tsohon Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi.
Ya kuma dogara da dokar ne wajen sake naɗa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II na 14 da Ganduje ya tsige a shekarar 2019 a matsayin Sarkin Kano na 16.
Sai dai wani basarake daga cikin masu zaɓar Sarki a Masarautar Kano Aminu Babba Danagundi, da Sarkin Dawaki Babba, sun kalubalanci dokar, inda suka bukaci kotun ta bakin lauyansa Chikaosolu Ojukwu (SAN) da ta soke ta.
Alkalin kotun mai shari’a Abdullahi Muhammad Liman bayan sauraron karar a zaman farko, ya dage zaman zuwa ranar Alhamis domin yanke hukunci kan karar.
Rundunar ‘yan Sandan Jihar Kano ta yi kira ga jama’a da su kasance masu zaman lafiya da kishin kasa yayin da kotu ta yanke hukuncin.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan Sandan SP Abdullahi Kiyawa ya fitar, ya nanata kudurin hukumar na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da gargadi kan duk wani yunkuri na tada rikici.
Tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro, rundunar za ta aiwatar da tsauraran matakan hana zanga-zangar jama’a da tarukan da ba su dace ba kamar yadda Gwamnatin Jihar ta kafa.
Masu tada ƙayar baya, da masu daukar nauyinsu za su fuskanci hukuncin shari’a, Za a tura isassun jami’an tsaro don tabbatar da doka da oda.
