Connect with us

News

Yadda Bankin Polaris Da Ma’aikacin Bankin Suka Sace Wa Kwastoma Naira Biliyan 16.5

Published

on

Bankin Polaris

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Shari’ar yadda Bankin Polaris da ma’aikacin bankin suka sace wa kwastoma Naira biliyan 16.5, ta koma hannun Antoni Janar na Tarayya

Advertisement

Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya karɓi aikin gurfanar da Bankin Polaris da wani ma’aikacin bankin a kotu, bisa zargin su da sace wa kwastoma Naira biliyan 16.5.

Za A Tsayar Da Albashin Alkalan Da Gwamna Abba Ya Nada Su Jagoranci Kwamitin Binciken Ganduje.

Ana tuhumar Bankin Polaris da da wani ma’aikacin bankin mai suna Chinenye Duru da laifin aikata zambar Naira biliyan 16.5.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa Antoni Janar na Tarayya ya karɓi gabatar da ƙarar daga hannun Sufeto Janar na ‘Yan Sandan Najeriya, wanda ya gurfanar da waɗanda ake zargin a cikin watan Disamba, 2023.

An yi zargin sun shafe tsawon shekaru takwas su na satar kuɗaɗen kwastoman daga cikin asusu-asusun ajiyar na bankin daban-daban.

Advertisement

‘Yan sanda sun bayyana sunan wanda aka riƙa satar wa kuɗaɗen da wani mai suna Onukogu Victor Hezekiah, Shugaban Cocin Living Christ Mission da ke garin Anacha, cikin Jihar Anambra.

Kwafen takardun gabatar da ƙara sun nuna cewa Bankin Polaris da Duru sun riƙa satar kuɗaɗen tun daga 2017 zuwa 2023. Shi Duru shi ne Jami’in kula da asusun ajiyar wanda suka ɗirka wa satar.

Advertisement

Ana gudanar da wannan shari’a a Babbar Kotun Najeriya da ke Legas, a ƙarƙashin Mai Inyang Ekwo, a Abuja.

Antoni Janar ya yi amfani da ƙarfin ikon da doka ta ba shi ta Sashe na 174(1) (b).

Advertisement

Sai dai ba a bayar da wani dalilin karɓe gabatar da shari’ar daga hannun Sufeto Janar ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending