News
Sarkin Kano na 16 ya taya Al, ummar musulmi murnar shiga sabuwar shekarar musulunci
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, yana farin cikin mika sakon taya murna ga daukacin al’ummar Kano dangane da samun nasarar kammala shekarar Musulunci ta 1445 da kuma shiga shekarar 1446 ta hijirar annabi muhammad (S A W)
Sarkin Ya Kuma ya taya zababben gwamna Jahar Kano alhaji abba Kabir Yusuf murna shigowar sabuwar shekara ta hijiriyya tare dayin addu,ar fatan zaman lafiya da kwanciyar hankalin da dukkan Al,ummar musulmin duniya
Sannan ya yabawa shugaban kasa, Nigeria Asiwaju Ahmed Bola Tinubu da Sarkin musulmin alhaji Sultan Abubakar Sa’ad wadanda yace sun sadaukar da kansu wajen ganin an samar da zaman lafiya da hadin kai da ci gaban al’ummar Musulmi Nijeriya baki daya
Sarki sunusi na biyu II yayi kira ga shuwagabanni na a kawo karshen rikice-rikice a tsakanin Musulmi da kuma yin amfani da bambancin ra’ayi na Nijeriya domin ci gaban dukkan ‘yan kasa a cikin shekara mai zuwa da kuma gaba.
Daga karshe kuma ya gargadi al’umma da su tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a lokacin bukukuwan sabuwar shekara ta Musulunci.
-
News7 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News3 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
