News
NDLEA Ta Kama Sarkin Gargajiya Da Kuma Wani Mai Hidimar Kasa Da Fataucin Kwayoyi A Kano
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa, NDLEA, ta kama wani matashi mai suna Yusuf Abdulrahman, mai shekaru 25, mai hidimar kasa, a karamar hukumar Sumaila ta jihar Kano, dauke da Loud mai nauyin kilo giram 1.250.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Femi Babafemi, Daraktan yada labarai na Hukumar NDLEA, ya fitar ranar Lahadi.
Shin Da Gaske Ne Ahmad Musa Ya Fice Daga Tawagar ‘Yan Wasan Nijeriya
A halin da ake ciki, sanarwar ta ce a jihar Osun, an kama shugaban al’ummar Akarabata a Ile-Ife, Ba’ale Ige Babatunde, mai shekaru 50, a ranar Juma’a 5 ga watan Yuli da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 5.
Yayin da yake yabawa jami’ai da jami’an runduna ta musamman da ke Osun, Benue, Ondo, Kano, da kuma babban birnin tarayya Abuja bisa kamawa, Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (Rtd) ya lura da kokarin da suke yi na rage samar da magunguna daidai da ayyukan wayar da kan jama’a na WADA yayin da ya umarei su da ‘yan uwansu a duk fadin kasar nan da su kula da lokaci.
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
