Connect with us

News

Wata Mata Mai Juna Biyu Ta kashe mijinta kan ƙaramin siket

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Rikicin da ya ɓarke tsakanin wani mutum da matarsa mai  juna biyu kan wani ƙaramin siket da matar ta saka ya yi sanadiyyar mutuwar mijin.

Advertisement

Matsalar ta afku ne da daddare lokacin da mutumin mai suna Patrick John ya dawo gida daga mashaya, inda ya haɗu da matarsa mai ciki sanye da ƙaramin siket, wanda a baya ya gargaɗe da ta daina sakawa.

Ma’auratan na zaune ne a ƙauyen Faram Faram ne a ƙaramar hukumar Fufore da ke Yola a Jihar Adamawa.

Advertisement

Jaridar DAILY POST ta ruwaito cewa a ranar Litinin 13 ga watan Yuni, 2024, a wani rikici da ya ɓarke, mutumin ya ƙalubalanci matarsa kan ɗan ƙaramin siket, inda aka ce ya shaƙe mata wuya, lamarin da ya sa matar ta yi ƙoƙarin ceton ranta.

Makwabtan da suka ji hayaniyar sun shigo da sauri suka raba su, amma mutumin ya bar wurin ne kawai ya dawo ya sake shaƙo matar kamar yanda Jaridar Blueprint ta ruwaito.

Advertisement

Matar mai suna Maryam, an ce ta ɗauko fartanya ne ta tafka wa mijinta a goshi, wanda hakan ya sa aka kai mutumin asibiti, inda daga baya ya mutu.

Maryam wadda ta gurfana a gaban kotu kan lamarin, ta kare kanta, inda ta ce ta yi halan ne domin tsira da ranta.

Advertisement

A babbar kotun majistare ta 2 da ke Yola, ƙarƙashin jagorancin Alƙali Musa Alhaji Adamu, Maryam ta danganta matakin da ta ɗauka da wani yunƙuri na kare kanta ba tare da ɓata lokaci ba.

Alƙalin kotun ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare ta bayan ta amsa laifin da ake zargin ta da aikatawa na kisan kai kuma ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 10 ga Yuli, 2024.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending