News
Ma’aikatar jami’o’i a Nijeriya sun shirya yin zanga-zanga a fadin kasar
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Ma’aikatan jami’o’i a Nijeriya, sun ce zasu fara zanga-zanga a fadin kasar daga ranar Alhamis 18 ga watan Yuli, 2024, kan albashinsu da suke bi na tsawon watanni 4.
Biyo bayan kasa cimma matsaya tsakanin ministan ilimi da na kwadago da kwamitin hadaka na kungiyoyin ma’aikatan jami’a, kungiyoyin biyu sun umarci mambobinsu su shirya zanga-zanga a fadin kasarnan.
Zanga zangar, acewar sanarwar da kungiyoyin suka rabawa shugabanninsu na shiyoyi da manema labarai za ta fara ne daga gobe Litinin 8 ga watan Yuli a fadin jihohin Najeriya ciki har da Abuja.
Sanarwar wacce ke dauke da sa hannun Sakatare janar na kungiyar NASU da na SSANU, Prince Peters Adeyemi da Comrade Mohammed H Ibrahim ta ce “Kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin NASU da SSANU ya gana a ranar Alhamis 4 ga watan Yuli na 2024 don daukar mataki kan rike albashin watanni 4 na mambobinmu”.
” Haka kuma kwamitin ya amsa gayyatar karamin ministan ilimi da sauran manyan jami’an gwamnati, sai dai tattaunawar bata nuna cewa za a biya albashin na watanni 4 ba da kuma sauraron kokenmu”.
Haka kuma kungiyar ta koka kan rashin ganawa da karamar minisatar kwadago kan batun.
A don haka kungiyar ta umarci mambobinta da su hada kansu a ranar Litinin tare da gudanar da zanga-zanga a ranar Talata.
-
News7 days ago
Gwamnatin Kano Ta Umarci Masu Talla Da Masu Sana’ar Jari Bola Su Bar Karkashin Gadar Tal’udu
-
News3 days ago
Ban Taɓa Nadamar Adawa Da Yunƙurin Obasanjo Na Wa’adin Mulki Karo Na Uku Ba — Atiku
-
News3 days ago
Jami’an Ƴansanda Sun Ƙwato Na’urorin Solar 160 Da Darajarsu Ta Kai Kimanin Naira 59.2 A Kano
