Connect with us

News

Gobara Ta Ƙone Rijiyar Kamfanin Man  NNPCL

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Hukumar kula da tace man fetur ta NUPRC, ta ce sun samu rahoton kamawar gobara a rijiyar Akaso mai baki huɗu da kamfanin NNPC ke gudanarwa a ranar Asabar.

Advertisement

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Laide Shonola ya fitar a ranar 3 ga watan Agusta ta ce, lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:12 na dare a ranar Juma’a inda gobarar ta faɗaɗa zuwa rafin da ke kusa da wajen.

Ba Ma Zabar Mutanen Da Za Su Yi Mana Hidima Muna Zabar Shugabanni Ne Waɗanda Za Su Bamu Taliya  – Shehu Sani  

Shiyyar gudanarwa ta 18 ta NNPC ta tabbatar da cewa an samu ɗaukin gaggawa domin kashe gobarar da kuma keɓance wajen ta hanyar amfani da wasu sinadarai da ke hana bazuwarta zuwa wasu wurare.

Advertisement

Haka nan, sanarwar ta ce su na ƙoƙarin maye gurbin man da aka rasa inda tuni su ka aika jirgin ruwan kamfanin da kuma jami’an sanya ido domin kulao da yanayin wajen.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Kawo yanzu dai, ba a gano dalilin aukuwar lamarin ba wanda a halin yanzu ta naɗa kwamitin bincike da ya ƙunshi masu-ruwa-da-tsaki domin gano musabbabin aukuwar lamarin.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Blueprint

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending