News
Zanga Zanga: Muna Allah Wa-Dai Da Kashe Mutane A Kurna Da Rijiyar Lemo, Da Sharaɗa A Kano —Kungiyar WAI
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kwamared Umar Ibrahim Umar, shugaban ƙungiyar War against Injustice ya ce suna Allah wa-dai da kashe mutane a Kurna da Rijiyar Lemo, da Sharaɗa a Kano, da sauran sassan Najeriya
Muna matukar bakin ciki da asarar rayukan da ba su ji ba ba su gani ba, da kuma amfani da karfi a kan ‘yan kasa da suke amfani da ‘yancinsu na asali da na dimokradiyya.
Simintin Dangote Ya Samu karuwar Kudaden Shiga A Kasuwannin Afrika
Muna kira ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki da su gaggauta binciki wadannan zarge-zarge tare da daukar matakin da ya dace kan masu aikata laifin.
Muna kira ga masu ruwa da tsaki da su ba mu hadin kai wajen neman adalci ga wadanda abin ya shafa da iyalansu. Muna neman a ba da cikakken bayani kan rayukan da aka rasa da kuma jikkatar da aka samu a lokacin zanga-zangar.
Yin amfani da karfi kan masu zanga-zangar lumana cin zarafi ne da take hakkin bil’adama da ‘yancin walwala. Za mu ci gaba da bayar da shawarwarin kare wadannan hakkoki tare da neman a gurfanar da wadanda ke da hannu a wannan ta’asa.
Muna mika ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda abin ya shafa tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
