News
Ya Kamata Shugabannin Nijeriya Da Yawa Su Kasance A Gidan Yari —Obasanjo

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ce galibin wadanda ke rike da mukaman gwamnati a Najeriya ba su da halin shugabancin kasar.
Ya kara da cewa kamata ya yi a ce sun kasance a gidan yari a halin yanzu.
Haɗarin Jirgin Sama Yayi Sanadiyar Mutuwar Mutane 62 Da Ke Cikin Jirgin
Obasanjo ya yi wannan jawabi ne a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun, yayin da ya karbi bakuncin ‘yan majalisar wakilai guda shida wadanda ke rajin kudirin wa’adin mulki na shekara shida, da na karba-karba na shugabancin kasa tsakanin arewa da kudu da kuma karba-karba na takarar gwamna daga cikin gundumomin sanatoci uku na kowace jihohi 36.
‘Yan majalisar dai sun samu jagorancin Ugochinyere Ikenga mai wakiltar mazabar Ideato ta Arewa da Ideato ta Kudu a jihar Imo.
Obasanjo ya dage cewa yayin zaben shugabanni, al’amuran dabi’a, ingancin da ya ce yawancin ma’aikatan gwamnati ba su da shi.
Manomin na Ota ya ce bayan sake duba dimokuradiyyar Najeriya, akwai bukatar duba shugabanci mai nagarta.
A cewarsa, har sai shugabanni sun sauya tunaninsu kasar ba za ta taba ganin canjin da ake bukata ba.