News
Gurin Allah Muke Nema —Hon Anas
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Dan takararar Kansila a mazabar Fulatan dake karamar hukumar Rogo Honorable Anas Garba Fulatan ya ce gurin allah muke nemai domin allah shine mai bada mulki ga wanda ya keso.
Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa, yayin da a ke tunkarar kakar zaɓen Shugabancin kanan Hukumomi da na kansiloli a jihar kano ƴan takara da dama na Jamiyyar NNPP a karamar hukumar Rogo na nuna buƙatar su ta tsayawa domin wakilci na al’ummar karamar hukumar su.
Ya Kamata Shugabannin Nijeriya Da Yawa Su Kasance A Gidan Yari —Obasanjo
Sai dai kuma, rahotanni na nuni da cewa kawo yanzu, ba a ga wata alama da ta nuna cewa dan takarar bazaiyi nassara ba a wannan lokacin.
Amma, a wani shirin tattaunawa da Jaridar INDA RANKA an jiyo Anas na cewa ita magana ta siyasa ko muƙami, gurin allah muke nemai domin allah shine mai bada mulki ga wanda ya keso.
A cewar Anas , ban da Allah, babu wanda zai iya baiwa wani muƙami, inda ya ƙara da cewa duk wanda ya kaɗai kugen siyasa da wuri ya san Allah ne ke yi, haka-zalika wanda ya jira sai nan gaba shima ya san Allah ne ke yi.
“Ita maganar siyasa ko maganar muƙami, kowa dai ya san Allah ne Ya ke yi. Banda Allah ba bu mai yi kuma a Jira kwai lokaci.
“Wanda ya buga kugen sa da wuri ya sani, wanda kuma ya bari ya jira lokacin Allah, shima kuma
ya sani.