Connect with us

News

Dalilan Da Ya Hana Ni Magana A Kan Rikicin Masarautar Kano – Ibrahim Shekarau

Published

on

Dalilan Da Ya Hana Ni Magana A Kan Rikicin Masarautar Kano Ibrahim Shekarau
Sardaunan Kano kuma tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Sardaunan Kano kuma tsohon gwamna Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana dalilan da suka hana shi magana a kan rikicin masarautar kano duk da cewa lamarin ya ya dame shi, amma ba ya son shiga cikin lamarin.

Advertisement

Tsohon gwamnan, ya baiyyana hakan ne a cikin gidan talabijin na Channels TV’s a shirin Politics Today, inda ya dora laifin rikicin a kan ‘yan siyasa.

Gurin Allah Muke Nema —Hon Anas 

Wanda hakan ya haifar ga samun sarakuna biyu tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi na 2.

Advertisement

Shekarau yace a matsayinsa na tsohon gwamna kuma babban ‘dan majalisar Sarki, yana matukar damuwa da halin da ake ciki, amma saboda ya na daya daga cikin manyan jihar bai dace yace komai ba, tunda maganar na gaban kotu.

Shekarau ya zargi ‘yan siyasa da haifar da matsalar da aka samu. Tsohon gwamnan yace da ‘yan siyasa sun nesanta kansu daga matsalar da bata kai haka ba. Shekarau ya bayyana fatarsa na ganin an warware matsalar cikin gaggawa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending